ZAHRAN BABA Complete Hausa Novel

 
 Garin gaya, garine mai cike da tarihi, wanda yake a k'ark'ashin jihar kano, garine wanda ake kasuwanci sosai, kuma ilimi na addine shine gaba, duk da basu damu da na boko ba, amma zaka same su, cikin wayewa Kowa yasan, Gaya ba mummuna, garine kuma, mai d'unbin tarihi, wanda Mutanen cikin garin kowa yasan mutane ne na gari, masu wadatar zuciya
K'auyene mai cike da, kyau, balantana yanayin damina, ko ina ka duba zaka sameshi garai garai ga ciyayi koraye, ga kayan gona duk sunyi, rayuwar mutanen abin sha'awa ce sosai
 Malam Aminu, shine babban malami, acikin garin, kuma yakasance babban liman na fad'in garin na Gaya, yanada almajirai da
yawa, saboda shahararsa hardaga k'etare na k'asa ana kamasa yara
Mutum nai mai kirki, kuma dattijon arzik'i, bafulatanine, farine tas, da farin gemun sa, Malami mai almajirai, kusan a k'asar
Hausa, zaka samesu al Qur'an, kawai su keda ilminsa
Amma, Malam ilmin Qur'an, fiqh, Tauheed duka ya had'a, da safe ana karatun al'Quran, da yamma kuma sai ayi na, Fiqhu da
Tauheed
Malam bashi kad'ai yake karantar dasu ba, akwai d'aliban da ya yaye, wad'anda ayanzu su suke taimaka masa, tareda manyan
'yayansa
Malam yanada Matan aure guda 4, uwar gida gwaggo Aneesa, sai ta biyu Inna Nafee, sai ta uku, Iya Hauwa, sai k"aramar cikin su
Yafando Aisha Uwar gida, tanada yara 6 Maza biyar sai mace d'aya, ta biyun tanada yara 5, Maza biyu, mata uku, sai ta uku, tanada yara biyar 5
Maza biyu itama mata uku
Sai Amarya wadda, takasance itama bafulatana ce, a yola malam ya aure ta, takasance 'yar babban liman nagarin yola
Bazawara ya aureta, tayi auren fari, Allah yayiwa mijin rasuwa, lokacin da malam yaje yola, anan ya ganta, kuma ya nuna
sha'awar aurenta, Aka bashi ita
Matan malam matane nagartattu, babu wanda ya tab'a jin Kansu, kuma malam a tsaye yake akan iyalansa
Babu raini ga k'anana akan manya, kuma manya babu raini ga Matan mahaifin su, idan har bakasan 'ya'yan kowacce ba, bazaka
tantance kace ga d'an wannan d'akin ba
Malam ya kasance mutum attajiri, ko almajiransa, basa bara, saboda sune suke masa aikin gona, shikuma yasakamusu da abinda
zasu ci(sab'anin malaman yanxu, da almajirai suke musu komai, amma lomar abinci basa basu)


Post a Comment

Previous Post Next Post

Post Ads 1

Post Ads 2

Advertising Space