YARIMA SUHAIL COMPLETE Hausa Novel

Hausa Novel download,Hausa Novel document,hausa Novel PDF download,hausa Novel PDF,hausa novel document

garin gazban garine mai albarka da yawan mutane yana d'aya daga cikin garuruwan da ake alfahari da su.sun kasance suna da babbar Masarautar da babu kamarta wajen girma da kyau  sarkin garin ya kasance sarki mai adalci duk kud'in mutum bai isa yazalunci nak'asa da shi ba indai har yazalunta labari yazo ma sarki toh sai yad'auki mataki, sarki umar yana son talakawansa sosai suma suna sonsa abun mamaki wannan sarki ya manyanta domin zai kai shekaru 76 ammah indai ba ka saniba sai kad'auka d'an shekara 50 ne,  domin babu alamun tsufa a tare da shi idan dukiyarce ya tara,  idan sarautarce yana d'aya daga cikin manyan sarakuna kai intabbatar muku wannan babbar Masarautar ko da me kazo anfika. 

Sarki faruk matarsa d'aya dattijuwa dada,  saidai abun mamakin duk mulkin nasa ammah 'ya'yansa biyu dukansu maza ne Ahmad shine babba sai k'anensa Abbas sun taso atare sun kasance suna son junansu. 
saidai a tsarin mulkin garin indai sarki yahaura shekaru arba'in (40) saman karagar mulki toh d'ansa ba zai ta6a gadon mulkinba saidai babban jikan gidan, saidai idan babu jika namiji shine d'an sarkin yake hawa mulkin lokacin da 'ya'yansa suka tasa yaza6a musu mata inda Ahmad ya auri d'iyar sarkin agadaz wato sultana Bilkisu,  shi kuma Abbas sarki ya aura masa  d'iyar d'an uwansa da yamutu yabari wato Sultana Sadiya. 

A cikin babbar Masarautar kowa aka fitar masa da 6angarensa. 
Suna zaune lafiya da matansu,  inda sultana Bilkisu takasance macece mai hak'uri da tawakkali ga ta macece mai kyauta ta kasance mai son jama'a,inda Sultana Sadiya takasance akasin haka domin bata son talakkawa suna ra6arta dan ma mijinta a tsaye yake sun d'auko hali irin na mahaifinsu, ammah duk da haka taci alwashin ita take da burin tafara haihuwar d'a namiji. 
saidai kash sultana Bilkisu ita tafara samun ciki, hankalin sultana Sadiya ya tashi sosai ganin ita ko 6atan wata bata ta6a yiba,
Bayan wata goma sultana bilkisu tahaifi d'iyarta mace murna wajen iyayen ba'a magana hatta ita kanta sultana Sadiya tayi murna ganin ba namiji bane ta haifa. 
ranar suna anyi shagali sosai kud'i sunyi kuka tsakanin masarautar gazban da masarautar agadaz anzuba naira sosai a inda yarinya taci sunan dada wato Asma'u ammah ana kiranta da husna.
 
Bayan shekara ukku Sultana bilkisu tak'ara haihuwa inda tasamu d'anta namiji kyakkyawa domin ita yabiyo kamar antsaga kara murna wajen su sarki ba'a magana hatta su kansu jama'a sun shaida wannan haihuwar domin sarki sadaka yadinga yi da dukiya sosai, akasin sultana Sadiya da takasa 6oye bak'in cikinta turakar mijinta taje tasameshi a zaune yana ta kiran waya yana fad'a ma mutane,  zama tayi gefensa tana kallonsa cike da takaici har yagama wayar sannan yakalleta fuskarsa d'auke da murmushi yace sultana akwai abinda kike buk'ata ne? 
sultana sadiya d'auke fuskarta tayi daga kallonsa tace ranka yadad'e meyasa kake murna dan matar d'an uwanka ta haifi namiji kar fa kamance shine zai hau karagar mulki bayan ran sarki, da mamaki sultan abbas yake kallonta yace sultana ba dai bak'in ciki kike ma d'an uwana ba dai ko? 



 

4 Comments

Previous Post Next Post

Post Ads 1

Post Ads 2

Advertising Space