EZNAH Complete Hausa Novel


Dattijo ne 'dan kimanin shekaru hamsin zuwa sama fari sol dashi Wanda kallo 'daya zakayi Masa ka tabbatarda
cikakken bafulatani ne,
Zaune yake kan tabarma a tsakar gidansa Yana kallon Mai 'dakinsa cikin farin cikin yanda take gyaran shinkafar daya
siyo Dan kawai a girkawa 'yar gaban goshinsa abincin tarbanta na dawowa daga makaranta data share watanni acan.
Da sallama wani 'dan madaidaicin saurayi yashigo hannunsa riqeda baqar Leda ya miqawa innarsu Yana cewa,
Baffa wlh yau kifi yayi wuya daqyarma nasamo wannan 'din sauran abari gobe da sassafe kafin su iso nakoma nagani
ko za'a samo.
Fuska cikeda annuri baffan yace,
Ba komai jafar wannan 'dinma zai Isa tunda goben nace aliyu ya Kama kaza biyu ya yanka Mata taci iya cinta.
Girgixa Kai inna tayi cikeda mamakin baffan akoda yaushe da baya iya danne fificin soyayyar _*ANANO*_ acikin
ransa duk garin ansan soyayyarta daban take aransa akan sauran 'yayansa.
Baffa salisu shine cikakken sunansa Kuma haifaffe Dan asalin qauyen 'danja qarqashin wata qaramar dake cikin jahar
yola.
Baffa nada Mata 'daya da 'yaya biyar ha'du maza Sai 'daya mace Wadda 'yan biyune aka haifesu Amma husainar
takoma tun kafin suna Sai aka barta da sunanta na _HASSANA_ Amma suna kiranta da _ANANO_ ma'ana hassana
da fillanci.
Anano itace auta Kuma itace qaramarsu kasancewar ba'a haifetaba Saida duka yannenta suka girma Sai yazamto kowa
gidan ji yake da ita musamman baffan daya 'dauki tsananin so da qauna ya 'dora Mata kasancewar ita ka'daice yarinya
qarama a gidan Dan tuni yannenta suka Zama samari.

     Scroll down to download NOVEL

Baffa nada arzikin dabbobi daidai gwargwado hakama yanada gonarsa dayake noma duk shekara shida 'yayansa.
Kaf qauyen Babu Wanda yayi karatun Boko Banda noma da kiwo Sai kuwa karatun addini,
Yusuf shine babba Kuma mai 'dan hakr saidai idan yafara fa'da to yanada wuyar saki,
Aliyu shine Mai bin Yusuf Wanda shikuma akwai fa'da da zafin Rai musamman idan aka ta6asa shiyasa kowa bai cika
shiga sha'aninsaba,
Sai Usman wanda Shima akwai rashin ji da fa'da musamman akan anano dayake ganin tafara iya rashin kunya sbd
sakarcin shagwa6a.
Jafar shine Mai sanyi da hkr acikinsu musamman akan anano dayake tsananin jida ita shima duk da dai kaf 'dinsu suna
tsananin sonta Amma tafi shiri dashi matuqa danshi har dandali yake kaita tayo kallo sudawo gida.
Tunda ta taso take Jin son karatu aranta Wanda kullum firarta kenan da baffanta Wanda yayi niyya tareda alwashin
kaita makaranta saigashi cikin ikon Allah aka turo masu fa'dakarwa akan karatun Boko qauyen shine mutum na farko
daya yarda 'yarsa taje kafin aka samu wasu qalilan Suma suka amince Nan take aka fara Shirin makaranta suka fara
zuwa.
Suna gama primary acikin qauyen suka wuce bording secondary School dake can cikin babban garin adamawa.
Tunda tafara zuwa makarantar idanuwanta suka qara bu'dewa musamman sbd dama can anano akwai tsiwa da ilimin
iya fa'dar baqar magana Wadda ba'a fa'da Bata mayarba Koda kuwa mutum waye.
Wannan hutun dasuka koma sun Dade Dan kuwa Saida suka share kusan wata biyar acan kafin suka fara shirye
shiryen dawowa Wanda sun gama karatun kenan.
Tunda jafar yaje yadawo yasanarda dawowarta ta gamo makaranta baffa da'di ya ishesa yafara shelar Ananonsa ta
gamo karatu zata Zama babbar likita Mai Duba mutane.
Nan take gari ya 'dauka musamman ma da'akaji Wai tazamo likita.
Shiri na musamman yasa ayi na tarbon Anano tareda murnar dawowarta Dan tuni aka fara zuwa tayasa murna tun
kafin ta qarason.
Anano farace tas tamkar 'yan gidansu saidai kaf tafisu kyau kasancewarta mace,
Ayanxu data kammala secondary 'dinta tanada shekaru goma Sha bakwai.
Koda dare yayi duk wani toye toye da gashe gashen kifi angama sbd ba abinda tafiso kamar gashashen kifi da albasa
tun tana qarama shiyasa harshi Saida baffa yasiyo aka gasa Mata.
Washe gari tunda safe yasa inna ta share ko Ina tareda 'dora girkin shinkafa harda miyar tumatir Wanda takanas sbd
ita yabada kudi aliyu yaje birni yasiyo shinkafar Dan adafa Mata.
Koda inna tagama aikin komai 'daki takoma ta kwanta sbd ciwon kan daya saukar Mata lokaci 'daya gashi Rana
hartayi yamma na nemanyi Amma shiru 'yan makarantar Basu isoba.
Kwance yake bakin swimming pool sanye da 3quater kawai cikin Yar qaramar rumfar shaqatawa dake gurin
idanuwansa a lumshe kamar Mai bacci Amma ba baccin yakeba farar fatarsa Sai wani kyallin hutu da kyau take
musamman dayake ba Riga ajikinsa.
Bu'de fararen oily eyes 'dinsa yayi ahankali tareda Kai hannu kan table ya'dau wayarsa akaro na ba adadi ya sake
Danna kiranta.
Switch off yakumaji ya tashi zaune zuciyarsa ba da'di sbd wannan karon shine karo na farko daya ta6a Kiran nafeesat
tun bayan aurensu Amma wayarta akashe.,
Miqewa tsaye yayi tareda sake Danna kiranta still akashe.
Kasa daina Kiran yayi Saida yajera Kiran kusan so ashirin Amma baya samu,,,
Hannuwansa ya zura a aljihun wandonsa tareda tsayawa bakin swimming pool'din ya qurawa ruwan Ido cikin tunani.
Tunda ya auri nafeesat tsawon shekara biyu kenan Amma bai ta6a 'daga waya yakirataba sbd kullum itace Mai kiransa
safe Rana dare harsai ya gaji ya kashe wayoyinsa sbd yanda yake damuwa da kiranta.
Sam Bata fushi da yanda baya kiranta itadai burinta takirasa taji ya yake,
Idan kuwa Yaje Yana tareda ita to batada Zama ta dingi hidimarsa Dan taga ta kyautata Masa ko Kuma taga
murmushinsa ko sau 'daya ne Amma bai ta6a ba.
Nafeesat nada haquri da juriyarda ba kowace mace ce keda itaba,
Wani irin so Mai qarfi na haqiqa take Masa Wanda tun farko yasa ya amince ya aureta sbd ta sadaukarda duk wani
farin cikinta akan soyayyarsa,
Bayan aurensu Bata tsinci komai ba Sai baqin ciki da rashin kula tareda halin ko inkula dayake nuna Mata Wanda tsill
ta danne sbd Bata ganin laifinsa ko ka'dan,
Tun kafin ta auresa harta auresa Bata ta6a ganin dariyarsaba kosau 'daya duk iya qoqarinta na ganin hakan bata
samuba sbd Babu so ko farin ciki dayakeji a rayuwarsa ko ka'dan,
Iya qunci zuciyarta na quntatuwa da yanda ta fahimci ba soyayyarta ko 'digo a zuciyarsa,
Tayi kuka a 6oye tayi a bayyane Amma takasa samun matsuguni a zuciyarsa duk da Yana soja Sam bayada zafin Rai
kamar na sauran soldiers shiyasa take qara tsananin sonsa sbd he's calm.

Scroll down to download NOVEL

Hakanan ta haqura ta fawwalawa Allah komai tacigaba da kyautata Masa Wanda sannu ahankali tsananin tausayinta
ya shigesa sbd hkr da tsananin qaunar datake Masa har Bata ganin laifi ko kuskuren duk abubuwan dayake Mata
musamman yanda ko Zama bai cikayi a qasarba.
Dawo da ita LA yayi gurinsa tareda tursasa zuciyarsa Bata kulawa,
Gwargwado yanayin iya qowarinsa gurin Bata kulawa da soyayya Wadda ita azahirin gskia tasan yanayi ne Dan ya
faranta ranta,
Cikin ikon Allah ahaka har ciki ya bayyana ajikinta,
Bata ta6a tunanin arayuwarta zatagansa cikin farin cikiba Saida yaji maganar cikin Wanda tun daga time 'din ya qara
ninka kulawarsa akanta sbd ayanxu Babu abinda yakeso sama da abinda ke cikinta sbd yanda rayuwarsa ke cikin
quncin rashin uwa,uba ko wani 'dan uwa dazai kalla yaji farin ciki Sai yanxu dazai samu 'dan kansa jininsa shiyasa
ahankali sonta da tausayinta suka fara samun kyakkyawan guri a zuciyarsa.
Tunda ta auresa ta gano qunci da ka'daicin da zuciyarsa take ciki ta maida dukkanin adduarta akan Allah yakawo farin
ciki Mai 'dorewa cikin rayuwarsa musamman data gano mum asee da qaninsa ba qaunarsa sukeba dukiyarsa suke
Hari.
Koda cikinta yafara tsufa ya maidata gida Nigeria sbd ta haihu acan bayan ya saka an 'dauko dattijuwar dazata kula da
ita duk da su mum na gidan.
Kullum itake kiransa tun asuba har dare Bata gajiya da Kira Koda bai 'daukaba saitabar Masa voice note Amma yau
akaro na farko da gari ya waye har Rana ta fa'di Bata kirasaba Wanda yasan tabbas Dole akwai mummnan dalilin daya
Hana Dan Bata yarda takasa kiransa komai rintsi.
Sake lumshe fararen idanuwansa yayi tareda qara 'daga wayar ya sake danna kiranta.
Same thing yakuma ji switch off,.

          DOWNLOAD NOVEL NOW

إرسال تعليق

أحدث أقدم

Post Ads 1

Post Ads 2

Advertising Space