AGOLAH Complete Hausa Novel by Nabila Rabiu Zango

  
Agarin kaduna, cikin unguwar Sarki. Awani katon gida, nashiga domin dauko maku labarin cikin gidan.
 Alhaji Abba Bala, hamshakin me kudine, yanada mata daya da ya,ya biyu mata, Sunan matarshi Hajiya Zarah, takasance yar
garin zariya, diyace agurin Malam Garba da matarshi Asabe, kishiyar mamanta, ce, tana kiranta da inna, Asabe takasance mace
me kissa, hakan yasa take zaune da Zarah tamkar ita ta haifeta, babu wanda yasan dalilinta nayin haka, talakawa ne acikin
danginsu kaf Zarah ce kadai tayi sa,ar auran me kudi, dalilin haduwarsu kuwa lokacin da Alhaji Abba yaje zariya acikin
unguwarsu Zarah, yaziyarci wani abokinshi, ahanyarshi ta dawowa yahadu da Zarah tadawo daga aiken da Innarta tayi mata,
lokaci guda yaji yakamu da sonta, ahaka. Bayan sungaisa yanemi data nuna mashi gidansu, yayi mata godiya yatafi.
Tundaga ranar soyayya tashiga tsakaninsu, kai tsaye yanemi izinin aurenta agurin mahaifinta, babu bata lokaci ya amshi
bukatarshi.
Zarah Allah yayi mata son kudi, babu abinda ta tsana irin talaka, duk da Allah yayita acikinsu amma bata son su, ko taron
danginsu akeyi bata shiga, hatta da iyayenta hakuri sukeyi da ita, tasha yin mafarkin ta auri me kudi, segashi Allah ya amsa mata
addu,arta tasamu me kudin,
 Zarah bata damu da ilimin addini ba, ko sallah bata damu dayiba, amma tunda suka hadu da Alh, Abba taboye duk wani halinta
marar kyau, shi kuma duk farin ciki ya isheshi yasamu diyar gidan mutunci, duk da azahiri iyayenta suna da mutunci amma bata
gado suba.
Ahaka akayi aurensu, aka kaita kaduna cikin unguwar sarki akaton gidanta, haka suka cigaba da rayuwarsu cike da so da kauna,
hankalinta ya kwanta, arzikin mijinta se karuwa yakeyi, hutu ya zauna mata tuni fatarta, ta murje tayi kyau sosai, tuni ta manta da
iyayenta da danginta, tunda akayi bikin bata zuwa garinsu sosai, sede idan mijinta ya matsa mata, shima sede suje tare kuma
bazata kwana ba, ko bikin dangine bata cika zuwa ba, idan ma yabata kudin gudummuwa ko kwatar abunda yabada bata basu,
gashi Allah yayi mata rowa.
Ahaka ta haifa mashi diyarta ta farko me suna Hauwa,u sunan mahaifiyarshice yasa dan duk iyayenshi sunrasu, dama shi kadai suka haifa, sede danginshi, hakan yasa aka sama diyarshi sunan mamanshi, ana kiranta da JIDDAH.

2 Comments

أحدث أقدم

Post Ads 1

Post Ads 2

Advertising Space